Halaye 3 da Budurwa ke nunawa Saurayi Idan tana Sonsa amma tana jin Kunyar Fada masa

0
539

Budurwar dake sonka a boye za ta yi wasu abubuwa da za su sa kasan cewa tana matukar kaunarka cikin sirri.

Za ta nuna ma wasu hanyoyi dake nuni da cewa tabbas ka mamaye zuciyarta. Babu budurwar da zata so ace ita ce ta fara furta kalmar so ga saurayinta sai dai za ta so ace shi ya fara bayyana mata so.

Anan ga wasu abubuwa guda 3 da budurwa ke yi idan tana son Saurayi kuma ta kasa fada masa;

1. A kodayaushe ta na so ta fada maka mafarkin da tayi.

Budurwar dake sonka zata nemi wata hanya ta boye da zata sanar da kai cewa tana tunaninka. Idan budurwa ta fadama ka cewa tayi mafarkinka, ta na fadamaka cewa ta damu da kai kuma tana son farin cikinka.

2. Tana yin kuka a duk sanda ka fada mata magana mai zafi.

Tana daukar kalamanka da mutunci, don haka duk lokacin da kayi mata wata magana mara dadi tana sanyata kuka saboda tana sonka. Kar kayi mata magana da kakkausan lafazi.

3. Budurwar dake kiranka a waya cikin dare don kawai sauraron muryarka.

Duk budurwar da ta sadaukar da baccinta domin sauraron muryarka hakika tana sonka. Hakan na nufin kai na musamman ne a wajenta kuma tana tunaninka. Kana sanya ta annashuwa da farin ciki. Hakan na nuni da cewa tana sonka amma baza ta iya fada ma ba.

Don haka idan ka samu budurwar dake nuna ma irin wadannan halayen ka gaggauta bayyana mata cewa kana son ta domin kuwa itama tana sonka sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here