Gwamnatin Tarayya ta Umarci Civil Defence da su bada Tsaro a Makarantun Najeriya

0
82

 

Daga Safiya Usman

Gwamnatin tarayya ta Bukaci Rundunar Kare Fafararen Hula ta Civil Defence da ta Mayar da hankalinta wajen Kula Tare Da Tsare Makarantu afadin Najeriya Domin Kare Lafiyar Dalibai Dake Karatu a Sassan Kasar Baki Daya.

Wananan Bayanin Ya Fito ne Daga Bakin Daraktan Yada Labarai Na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Muhammad Manga aka Kuma Rabawa Manema Labarai a Birnin Tarayya Abuja.

Ministan Ya Bayyana Hakan Yayin da Yake Bikin Nada Ahmad Abubakar Audi Amatsayin Sabon Shugaban Rundunar Ta kasa Wanda ya Gudana a Birnin Tarayya Abuja.

Ya ce Gwamantin Tarayya ta Dauki wannan Mataki ne Domin Kare Lafiyar Daliban Daga Masu Garkuwa Da Mutane wadanda Ke Kai Hare Hare Ga Makarantu a Wasu sassan Kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here