Gwamnan Yobe ya Auri Gumsu Abacha cikin Sirri inda ta zama matarsa ta 4

0
401

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin Riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya auri yar gidan tsohon shugaban Najeriya, Gumsu Abacha cikin sirri, inda ta zama matarsa ta hudu.

Jaridar SAHELIAN TIMES ta rawaito cewa an yi takaitaccen bikin a gidan yayan Gumsu a watan Disamba.

A baya dai Gumsu Abacha ta taba auren dan kasuwarnan na kasar Kamaru, Bayero Fadil Mohammadou, kafin su rabu a shekarar 2020.

Wata majiya daga dangi ta shaidawa jaridar cewa Gumsu da Buni suna soyayya kafin a daura aurensu a Abuja.

Gumsu Abacha dai na da ‘ya’ya 5 da ta samu daga tsohon mijinta.

Gwamna Mai Mala yana kuma auren yar gidan tsohon gwamnan jihar ta Yobe, Sanata Ibrahim Geidam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here