Ƴan Bindiga Sun nuna Buƙatar Auren Ɗaliban Jangebe da suka Sace

0
253

Yan bindigar da suka ce yan matan makarantar Jangebe sun bawa yan matan lambobin wayoyinsu inda suka yi alkawarin ziyartar iyayensu don neman aurensu.

Daliban da dama da suka zanta da jaridar Daily Trust sun ce wadanda suka sace su sun nemi soyayyarsu inda suka ce idan sun koma gida su kirasu a waya idan sun amince zasu aure su.

Daya daga cikin yan matan mai suna Hassatu Umar Anka, ta ce yan bindigar sun shawarci daliban da su dena zuwa makaranta wanda hakan zai bada dama a aure su.

“Yayin da ake shirin sakarmu, wasu daga cikinsu sun zo wajenmu suna nuna mu suna cewa, ‘muna kaunar wasu daga cikinku kuma muna son aurenku idan zaku amince. Ku dena bata lokacinku kuna makaranta’, ” inji ta.

Ta ce, yan bindigar na matukar tsoron jirgin sojin Najeriya inda ta ce a duk lokacin da suka ji karar wani jirgi suna guduwa su buya.

“Sun yi jirgin yakin soja suna da ” Shaho” idan suka ga daya suna ce mana mu buya a karkashin kogo ko bishiya. Hakika yana basu tsoro”, inji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here