Sace Dalibai da Yan Bindiga Ke yi Karamin Laifi ne idan aka Kwatanta da Kashe Mutane – Sheikh Gumi

0
442

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana sace dalibai da yan bindiga ke yi a matsayin karamin laifi.

Sheikh Gumi ya ce sace dalibai karamin laifi ne idan aka kwatanta shi da kona garuruwa da kashe mutanen garin.

Ya bayyana hakan ne a tataunawarsa da BBC Pidgin.

Malamin ya kuma yi bayanin cewa, tattaunawar da yake da yan bindiga na haifar da kyakkwan sakamako yayin da yan bindigar a yanzu ke mutunta rayukan mutane.

A cewar Sheikh Gumi: “Sace yara daga makaranta karamin laifi ne saboda daga karshe dai za’ayi sulhu kuma yanzu yan bindga suna kula da rayukan mutane.

” Kafin haka, burin yan bindiga shi ne su je gari, su kone shi su kashe mutane, zan iya cewa wa’azin da muke yi yana amfanarwa kuma akwai fatan cewa karshen wadannan matsaloli na yan bindiga yazo a jihar Zamfara da wasu jihohi.

A yan kwankin nan dai yan bindiga na yawan kai faramaki tare da sace mutane a arewacin Najeriya.

Idan za’a iya tunawa dai, Sheikh Gumi ya roki gwamnati ta yi wa yan bindiga afuwa.

Malamin ya ce yiwa yan bindigar afuwa zai taimaka waje shawo kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya.

Kodayake shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa bazai saurarawa yan bindigar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here