Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun yi Yunkurin Kara Sace Dalibai a Jihar Niger

0
155

Yan bindiga sun kutsa makarantar kwalejin fasaha ta garin Kagara a karamar hukumar Rafi ta jihar Niger.

Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa, yan bindigar sun kutsa makarantar ne da daren ranar Lahadi amma basu samu kowa a makarantar ba.

Gwamnati ta rufe makarantu a yankin bayan sace dalibai da ma’aikatan makarantar Sakandire ta Kagara.

Yan bindigar da suka so sace dalibai da dama, rahotanni sun bayyana cewa sun bar makarantar cikin fushi, inda suka je wajen al’ummar dake kusa da makarantar tare da sace mutane 4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here