Hukumar JAMB ta Sanar da Ranar da za’a Kammala Bada Gurbin Karatu na Shekarar 2020/2021 a Manyan Makarantu

0
154

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa(JAMB) ta sanar da ranar 15 ga Yuni a matsayin ranar karshe ta kammala bayar da gurbin Karatu na shekarar 2020 a manyan makarantun Najeriya.

Gurbin karatun na jarrabawar samun gurbi karatu ce da aka gudanar a shekarar da ta gabata.

Hukumar ta fitar da sanarwar ne a safiyar yau Lahadi.

Sanarwar ta ce, “Za’a kammala dukkan al’amuran da suka shafi bayar da gurbin karatu na shekarar 2020/2021 a manyan makarantun Najeriya a ranar 15 ga watan Yuni na shekarar 2021.

“An dauki matakin ne bayan taron da aka gudanar da shugabannin makarantu ta kafar Internet ranar Laraba 24 ga watan Fabarairu.”

A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaban hukumar ta JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce taron da aka gudanar da makarantun anyi shi ne don sanin matsayar da za’a cimma kan batun tsarin bayar da gurbin karatu na shekarar 2020/2021.

A taron an amince cewa, manyan makarantu na gwamnati zasu kammala bayar da gurbin karatu kafin ko ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 2021, yayin da makarantu masu zaman kansu da kwalejojin fasaha da na ilimi za su kammala a ranar 15 ga watan Yuni na shekarar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here