An yi Kira ga Ƴan Jarida kan su dinga Bin Matakan Kariya daga Cutar Korona

0
133

 

 

Daga Safiya Usman

Anyi kira ga ‘Yan jarida a jihar Kano da su kasance masu kiyaye ka’idojin kaucewa kamuwa da annobar Korona.

Shugaban kungiyar ma’aikatan Rediyo da talabijin da al’adu ta kasa, wato RATTAWU , Comrade Dakta Kabir Garba tsanni shi ne ya yi wannan kiran yayin bikin kaddamar da rabon takun kumin rufe hanci da baki da akafi sani da face mask wanda kungiyar reshen jihar kano ta Samar domin rabawa ‘ya’yanta da ya gudana a sakatariyar kungiyar dake a rukunin gine-gine na baje koli.

Ya ce bayaga ma’aikatan lafiya, ‘Yan jarida su ne kan gaba gurin fuskantar hadarin kamuwa da cutar, adon haka ya ja hankalinsu gurin yawaita wanke hannu da sanya takunkumin na baki da hanci.

A jawabinsa tunda fari shugaban kungiyar ta RATTAWU reshen jihar Kano Comrade Abubakar Garba Macchido ya ce, kungiyar na iyaka kokarinta gurin wayar da kan ‘ya’yanta akan yadda zasu dauki matakan kariya musamman a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Kungiyar ta RATTAWU dai ta Samar da takunkumi da sinadarin wanke hannu na sanitizer wanda za ta rabawa ‘ya’yan kungiyar a sasaan jihar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here