An bayyana Waɗanda Za su yi Alkalanci a Muƙabalar Abduljabbar da Malaman Kano

0
291

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, Muhammad Tahir(Baba impossible) ya bayyana cewa , Farfesa Shehu Galadanchi da limamin Kano, Farfesa Zaharadden ne zasu kasance alkalai a mukabalar da za’ayi tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano wacce za’ayi ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2021.

Jaridar SAHELIAN TIMES ta rawaito cewa, Sarkin Musulmai, Sa’ad Abubakar III, zai kasance babban bako a taron mukabalar.

An baiwa malaman Kano dama su zabi malaman da za su kara da Abduljabbar Kabara kan wasu batutuwa guda 9 wadanda Abduljabbar zai yi karin bayani a kansu.

Sannan an gayyaci malamai da dama daga wajen Kano kuma za’a gudanar da mukabalar ne a fadar Sarkin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here