Abubuwa 4 dake Sanya Yan mata Kamuwa da Soyayyar Saurayi Cikin Sauri

0
773

A wanan makalar zamu fahimci wasu abubuwa kalilan da budurwa zata gani tare da saurayi taji ta kamu sa son shi da sauri.

Abubuwan su ne:

1. Yan mata na saurin kamuwa da soyyayar Saurayin da yake kwalliya, yawancin yan mata na son saurayin da ya iya sa kaya, matukar kana da cikin samarin da suka iya ado da kwalliya tabbas yan mata za su soka cikin sauki.

2.Wani abu dake sanya budurwa jin soyyayyar Saurayi ta shiga ranta shi ne yayin da saurayin ya kasance mai bada dariya, yawan yan mata na son saurayin da zai dinga sanya su dariya a lokaci da dama.

3. Idan kai Saurayi ne kuma a kodayaushe kana cikin kamshi, kana sanya turare hakan zai sa yan mata su soka.

4. Yayin da kake hira, kuma kake warware abubuwa cikin kwanciyar hankali, babu hayaniya ba fada, kana gamsar da budurwarka abinda yake dai-dai, wannan halayya nasa yan mata suji suna kaunar Saurayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here