Yanzu-Yanzu: Muna tsare da Salihu Tanko Yakasai – DSS

0
214

Hukumar tsaro ta farin kaya(DSS) ta tabbatar da cewa ta tsare tsohon mataimaki ga gwamna Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakasai.

Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya ta DSS ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar yau Asabar.

“Muna tabbatar da cewa Salihu Tanko Yakasai yana tare damu. Ana bincikarsa kan batutuwan da suka shafi bayyana ra’ayi a shafukan sadarwa na zamani ba bisa ka’ida ba” inji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here