Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Rufe Wani Kamfanin Shinkafa dake Sharada

0
235

Gwamnatin jihar Kank ta kulle wani kamfanin Shinkafa dake Sharada mai suna Al-Wabil tare da cin tararsu Naira Dubu Dari Biyar biyo bayan samun su Suna Gudanar da Aiki sa’ilin da ake Sharar Tsabtar muhalli na Karshen Wata wata.

 

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano Dr kabiru Ibrhaim getso,  shi ne ya Bayyana Haka sa’ilin da yake jagorantar tawagar dake zagayen duba garin a wannan rana ta Asabar.

Kwamishinan yakuma Kara da cewar Gwamnati ba za ta kyale Duk wani mutum dake yunkurin Karya Dokar ta ba musamman ma a lokacin tsaftar muhalli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here