Jerin Sunayen Manyan Makarantun da Gwamnatin Jihar Kano ta bada Umarnin Rufewa

0
97

Daga Junaid Idris Gezawa

Gwamnatin jihar kano ta bada umarnin rufe wasu manyan makarantun jihar nan take sakamakon matsalar tsaro a fadin kasarnan kamar yadda sanarwar da dakta Mariya Mahamoud Bunkure, kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta bayyana

Makarantun da abin ya shafa sune:

1. RMK college of Advanced and Remedial Studies T/Wada.
2. School of Environmental Studies Gwarzo.
3. School of Rural Technology and Entrepreneurship Dev ( SORTED) Rano and
4. ABCOAD

Gwamnatin ta jihar kano ta bada Umarnin rufe makarantun ne biyo bayan sace wasu dalibai a sassa daban na Arewacin kasarnan.

Haka kuma, biyo bayan wannan umarnin, ana umartar dukkan ɗaliban makarantun da abin ya shafa dasu fice daga Makarantun da wuri-wuri har sai gwamnati ta bada Umarnin sake bude makakarantun anan gaba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here