Allurar Rigakafin Cutar Korona zai Iso Najeriya Ranar Talata – Boss Mustapha

0
126

Gwammatin Najeriya ta tabbatar da cewa allurar rigakafin Korona guda Miliyan 4 na AstraZeneca zai iso kasarnan da safiyar ranar Talata.

Shugaban kwamitin yaki da Korona na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a wani Bidiyo da ya aikewa jaridar PREMIMUM TIMES a daren jiya Asabar.

“Ina tabbatar muku cewa, rigakafin na nan zuwa, suna nan zuwa da sauri.

“Mun amincewa cewa allurar rigakafin zata taso daga kasar India a ranar 1 ga watan Maris da karfe 10:30 na dare, zasu iso Abuja a ranar Talata biyu ga watan Maris da karfe 11:10 na safe”.

Najeriya dai na tsammanin samun rigakafi miliyan 16 na Astrazenaca ta hanyar shirin raba allurar rigakafin Korona biliyan biyu da hukumar lafiya ta duniya ta bullo dashi ga kasashe masu rauni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here