Sace Ɗalibai: “Gwamnatin APC ta Gaza a Kowanne Mataki”- Inji Hadimin Ganduje

0
1032

Salihu Tanko Yakasai, mataimaki na musamman ga gwmana Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano kan kafafen yada labarai ya ce gwamnatin APC ta bawa yan Najeriya kunya.

Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yau Juma’a yayin da yake mayar da martani kan sace daliban makarantar Sakandiren Jangebe dake Talata Marafa a jihar Zamfara.

Yan bindiga dai a safiyar yau Juma’a sun farwa makarantar tare da sace dalibai sama da 300.

A martanin da ya mayar, Salihu Tanko Yakasai ya ce, abin takaice ne ace an sake sace dalibai kasa da makwanni biyu bayan an sace daliban Kagara.

Ya ce lamarin tabarbarewar tsaro a kasarnan na nuni da cewa gwammatin APC ta gaza wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.

“maganar gaskiya, gwamnatinmu ta APC a kowanne mataki, ta gaza a fannin da aka zabe mu na kare rayuka da dukiyoyi. Babu wata rana da zata zo ta wuce ba a samu irin wannan matsalar tsaro ba. Wannan abun kunya ne! Kayi maganin yan ta’adda yadda yakamata ko kayi murabus”, inji Salihu Tanko Yakasai.

Ya kara da cewa abun ya zama kamar al’ada a duk sanda irin wannan lamari ya faru, gwamnati bata daukar wani mataki don kare afkuwarsa anan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here