Sace Ɗalibai: Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Rufe dukkan Makarantun Kwana a Jihar

0
120

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bada umarnin rufe dukkan makarantun kwana a fadin jihar nan take biyo bayan sace daliba mata 317 a makarantar Sakandiren Jangebe.

Gwamnan ya bada umarnin ne a yau Juma’a a wani jawabi da yayi a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.

Yayin da yake jajantawa iyayen daliban da aka sace, gwamnan ya tabbatar da cewa za’a kubutar dasu.

Acewar gwamnan, an tura jirage jihar don tallafawa aikin ceto daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here