Osinbajo na son CBN ya Sauya Matakin da ya dauka na Haramta amfanin da Kudin Internet

0
87

 

 

Daga Junaid Idris Gezawa

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa,mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce “ya kamata” Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake duba matsayinsa na haramta amfani da kuɗin intanet a ƙasar wato cryptocurrency.

A farkon watan Fabarairu ne CBN ya haramta amfani da kuɗaɗen bisa dalilai na tsaro, yana mai cewa “ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma halasta kuɗin haramun”.

“Na gane hikimar da ta sa CBN da sauran hukumomi suka haramta kuɗin intanet, amma ina ganin ya kamata a sake dubawa,” in ji Osinbajo cikin wani bidiyo da mataimakinsa kan kafafen yaɗa labarai ya wallafa.

“Akwai rawar da dokoki za su taka a nan. Aikin hukumomi ne su sanya dokokin da za su daƙile waɗannan matsalolin ba lallai sai an salwantar da alganun da ke tattare da shi ba.

“Nan gaba kuɗin intanet zai kawo ƙalubale game da yadda bankuna ke aiwatar da ayyukansu ta hanyar da ba mu taɓa tunani ba.”

Najeriya na sahun gaba a cikin ƙasashen da aka fi mu’amala da kuɗin intanet a faɗin duniya.

A jiya Alhamis, masu amfani da shafukan zumunta a Najeriya suka harzuƙa sakamakon kalaman da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi cewa ba za su taɓa amicewa da kuɗin intanet ɗin ba.

Jerin kuɗin intanet da ake kasuwanci da su

  • Bitcoin
  • Ethereum (ETH)
  • Litecoin (LTC)
  • Cardano (ADA)
  • Polkadot (DOT)
  • Bitcoin Cash (BCH)
  • Stellar (XLM)
  • Chainlink
  • Binance Coin (BNB)

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here