Gwamnatin Buhari ba ta tallafa mana wurin ceto ɗaliban Kagara – Gwamnan Neja

0
189

Daga Junaid Idris Gezawa

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, gwamnan Jihar Neja a Najeriya Abubakar Sani Bello ya koka kan abin da ya kira “rashin taimako” daga Gwamnatin Tarayya game da yunƙurin ceto ɗaliban makarantar Kagara da aka sace a jihar.

Gwamnan ya koka cewa “babu alamun Gwamnatin Tarayya” a jihar domin ceto ɗaliban guda 27 da malamansu da ma’aikata 14 da aka sace ranar Laraba, 17 ga watan Fabarairu.

Ya bayyana haka ne jiya Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Sanata Orji Kalu, wanda ya kai masa ziyarar jaje.

“Ya zuwa yanzu dai, ba mu ji wata alamar Gwamnatin Tarayya ba a nan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Sufeto Janar na ‘yan sanda ya turo mana tawaga huɗu ta ‘yan sanda amma mu ne za mu ɗauki nauyinsu. Saboda haka ina taimakon? Babu wani taimako daga kowa.

“E, wakilai (na Gwamnatin Tarayya) sun kawo mana ziyarar jaje, amma maganar kenan. Saboda haka an bar mu mu kaɗai kawai.”

Ya ƙara da cewa duk da halin rashin taimakon da suke ciki, gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin ceto mutanen.

“Mun dage wurin ceto yaran nan cikin ƙoshin lafiya ko babu taimakon kowa,” a cewar gwamnan, wanda tun farko ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here