Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 a jihar Zamfara

0
202

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, rahotannin da BBC ke samu daga Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata fiye da 300 daga makarantar sakandiren GGSS Jangeɓe da ke jihar ranar Alhamis da daddare.

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan ‘yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

Haka kuma wani mutum da aka sace ‘yarsa daya mai suna Bilkisu da ‘ya’yan ‘yan uwansa biyu, ya ce daruruwan ‘yan bindiga ne suka isa makarantar inda suka soma da kai hari kan masu gadi kafin su yi awon gaba da daliban.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ‘yan fashin daji da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here