Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta yi Kira da a Kama Sheikh Ahmad Gumi Bisa Ƙage Ga Ƴan Jarida

0
263

Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya(NUJ) ta yi kira da a kama Sheikh Ahmad Mahmud Gumi bisa ƙage da yayiwa yan jarida cewa “masu aikata laifu ne” saboda suna kiran yan ta’adda masu laifi.

Kungiyar ta bayyana rashin gamsuwa da kalaman da Sheikh Ahmad Gumi ya yi yayin tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV, inda ya yi ƙage ga yan Jarida cewa suma masu laifi ne saboda suna kiran yan bindiga da masu laifi.

Malamin yayin zantawarsa da Arise TV ya ce,”Kana bayani a kan aikata laifuka, bansani ba. Hatta yan Jarida suma masu aikata laifi ne saboda suna kunna wutar rikici. Wadannan mutanen suna saurarenku, kar ku kira su masu laifi idan kuna so su dena abinda suke yi”, inji malamin.

“Matasa a shirye suke su ajiye makamansu, yanzu suna jinku kuna kiransu masu laifi, ta yaya kuke so su bada hadin kai. Don haka yakamata ku nuna musu cewa suma yan Najeriya ne, a hakanne baza su ci zarafin yara ba zasu kasance masu bin doka, wadannane kalaman  muke son ji daga yan Jarida da zai taimaka mana mu kubitar da yaran nan.

” Yayin da muka yi musu magana mai dadi, sun shirya ajiye makamansu, sun shirya sauraronmu, amma idan ana maganar aikata laifuka, kashe su, daure su, toh a haka zamu kare”, inji Gumi.

Kungiyar yan Jaridun ta ce gungun yan bindigar da Sheikh Gumi ke cewa ba yan ta’adda bane da kansu sun tabbatar da cewa yan ta’adda ne a yayin tattaunawarsu da dan jaridar nan Abdul’aziz Abdul’aziz.

Kungiyar ta ce, “Muna gayyatar Sheikh Gumi yazo yayi bayani ga yan Najeriya kan me yasa duk da ziyarar tattaunawar sulhu da yake da yan bindiga a jihar Zamfara, amma har yanzu yan ta’addan na ci gaba da kisa, sace mutane da yin fyade, ciki har da dalibai 300 da aka sace a jihar Zamfara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here