Kotu ta ci tarar Kakakin Rundunar Ƴan Sanda Reshen Jihar Kano

0
673

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano ta ci tarar kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, Naira Miliyan 1 bisa laifin cin zarafin dan adam bayan jami’an yan sanda sun tsare Bashir Bashir Galadanci, bisa zarginsa da sukar kakakin yan sandan a shafinsa na sadarwa.

Yan sanda sun kama Bashir Galandanci a shekarar da ta gabata inda suka tuhumarsa bisa bayanan da yake wallafawa a shafinsa na Facebook inda yake yabawa tsohon kakakin rundunar yan sandan, Abdullahi Majiya, a mafi yawan rubutunsa tare kuma da taba muhibbar Abdullahi Kiyawa wanda shi ne kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano a yanzu haka.

A hukunci da ya yanke, mai shari’a Obiora ya ci tarar DSP Abdullahi Kiyawa Naira Miliyan 1 bisa cin zarafi da tsare Bashir fiye da sa’o’i 48, ya take masa hakki. Kotun ta kuma ce Bashir yana da yancin fadin albarkacin bakinsa kamar yadda kundin tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.

Kotun ta ce yan sanda kar su kara gayyatar bashir ko kama shi kan wannan batu har abada sannan kotun ta nemi Abdullahi Kiyawa ya nemi gafararsa a gidan Rediyo bisa cin zarafinsa.

Sauran wadanda ake karar sun hada da : Inspector Abb Jakara, Imarana matukin kakakin rundunar yan sandan ta Kano, tsohon mai kula da sashin Anti Daba, Uba Bangajiya.

A tattaunawarsa da Jaridar SAHELIAN TIMES, Bashir ya bayyana yadda yan sandan suka tsare shi, suka dake shi tare da tilasta yayi karya ga tsohon kakakin rundunar yan sanda na jihar Kano, Magajo Musa Musa Majia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here