Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a Matsayin Shugaban Hukumar EFCC

0
90

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon hukumar EFCC.

Tabbatar da shi din na zuwa ne jim kadan bayan bayyana gaban majalisar domin tantancewa.

Yan’uwa da abokan Abdulrasheed Bawa ne dai suka raka shi zauren majalisar.

Sabon shugaban na EFCC mai shekaru 40 yayi aiki da hukumar tsawon shekaru 16 kuma kwararre ne wajen binciken almundahanar kudade.

A lokacin da ake tantance shi, Abdulrasheed Bawa ya tabbatarwa da yan majalisar burinsa na inganta ayyukan hukumar ta EFCC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here