WAEC ta Musanta batun cewa ta Riƙe Sakamakon Jarabawar Ɗaliban Kano

0
181

Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta yammacin Afrika(WAEC) ta musanta rahotan zargin cewa ta rike sakamakon jarranawar daliban jihar Kano saboda bashin da take bin gwamnatin jihar.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannub Demianus Ojijeogu, mai rikon mukamin shugaban sashin hulda da jama’a.

Ya ce babu kamshin gaskiya a rahotan.

Kamar yadda ya ce “domin kau da shakku hukumar na sanar da cewa ta saki sakamakon jarrabawar daliban Kano da sauran wadanda suka zana jarrabawar a ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba, 2020.”

“Gwamantin Kano bata rike bashin wannan hukuma ba. Kuma ba rike sakamakon jarrawabar daliban jihar ba kamar yadda aka yi zargi.

“Hukumar WAEC na yin kira ga gwamnatin Kano, Iyaye da makarantu da masu ruwa da tsaki su watsi da labarin”, inji Ojjeogu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here