Ra’ayi: “Wai Fa Ashe Nima Tsohon Mai yin doka Ne” – Musayyib Kawu Isah

0
178

 

Idan na tuna na taba zama mai yin doka abin yana bani dariya matuka da gaske. Abinda yasa nace haka kuwa shine; a zahirin gaskiya yan majalisa nada matukar muhimmanci wurin gudanar da mulkin alumma. Sune masu yin doka su mikawa bangaren zartsawa domin tabbatarwa.

Idan ance majalisa, ana nufin tun daga kan ta kansiloli dake kananan hukumomi, majalisar jiha da kuma ta tarayya. Suna da hurumin tsige Ciyaman, Gwamna da shugaban kasa idan sun aikata laifi, amma su kuma babu mai iya tsigesu saidai wadanda suka zabesu suyi musu kiranye.

Amma duk da wannan karfi da suke dashi a zahiri ya zama na banza tunda basa iya takawa bangaren zartaswa burki aduk lokacinda suke aikata wani kuskure bama sukai ga batun tsigesu ba.

Abinda ke kawo wannan kuwa ba komai bane sai zama yan amshin shata da majalisun sukayi. Tunda fari basa iya zabarwa kansu shugabanci sai abinda shugabanni suka zabar musu, shin ta yaya kuke tsammanin majalisun zasu iya tabuka wani abin kirki tunda basu da ra’ayin kansu?

Indai anaso muga daidai, ya zama wajibi a sakarwa majalisa damar gudanarda aikinta babu kutse. Ciyaman, Gwamna da shugaban kasa su zare hannunsu daga harkokin majalisa su kyalesu suyi aiki yadda kundin tsarin mulkin kasa ya basu dama.

Akwai lokacinda kiri kiri muka tsige shugaban majalisar kansilolin Ungogo muka maye gurbinsa da wani. Doka ta bamu dama a wancan lokaci mu cireshi koda beyi laifin komai ba. Amma haka muka samu turjiya daga bangaren Ciyaman harma da gwamnatin jiha wanda rigimar saida ta kaimu ga tafka mahawara gaban alkali inda daga karshe dai kotu ta bamu gaskiya.

Irin wannan kutsen bazai taba haifarwa da dimokaradiyyar kasar nan da komai ba sai koma baya. Da fatan za’a samu hanyar gyara a kyale kowa yayi aikinsa daidai da yadda doka ta tanadar indai muna bukatar ganin daidai a kasar nan.

Tsohon kansila a mazabar ungogo dake karamar hukumar ungogo,Musaiyyib Kawu Isa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here