Gwamna Zulum ya ce Ba zai Kori Fulani Makiyaya Daga Jiharsa ba

0
102

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ce Ba zai kori Fulani makiyaya Daga jiharsa ba sai dai ya ce zai samar musu da filin kiwo hekta 5,000 domin gudanar da harkokinsu na Kiwo.

Ya kuma kirayi sauran jihohin arewa da su duba lamarin samar da wuraren kiwo a jihohinsu.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya ce jihar Borno na da filin noma mai fadin kusan kilomita murabba’in dubu 73 wanda zai iya daukar makiyaya masu Taron yawa.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne yayin kaddamar da fara aikin gaggawa na Hukumar Kula da Yankin Arewa maso Gabas a Maiduguri

Zulum ya bayyana cewa, ya kasance yana goyon bayan samar da wuraren kiwo ga makiyaya a tsakanin jihohi shida na Arewa maso Gabas domin hakan zai samar da ci gaban tattalin arziki ba ga yankin ba kawai har da kasa baki daya sannan kuma zai bunkasa sha’anin kiwo a yankin. .

Ya ce, “Muna da filayen noma a nan Arewa maso Gabas. Na dade ina ba da fatawar a kirkiro da wuraren kiwo a yankin, Kuma nayi imanin Kowacce jiha a Arewa-maso-Gabas na iya samar da akalla hekta 5,000 na cibiyoyin kiwo inda za mu bunkasa kiwon dabbobi har miliyan biyu zuwa uku.” Inji gwamna Zulum

Gwamnan ya ce yayin da wasu ke korar makiyaya daga jihohin su da yankin su, jihar Borno za ta nemi samar da filaye don kafa cibiyoyin da za su taimaka wajen samar da dabbobi da kuma bunkasa ayyukan noma a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here