Ƴan Bindigar Kudancin Najeriya Sun Kashe Ƴan Sanda 4 tare da Ƙone Ofisoshinsu a Jihar Abia

0
115

Rahotanni sun ce yan bindigar Kudancin Najeriya sun kashe dan sandan dake rakiyar sakamakon zabe a jihar Ogun.

Bayanai sun bayyana cewa yan bindigar sun kashe jami’an yan sanda hudu a yau Talata tare da cinna wuta a ofishin yan sanda dake Abayi Osisioma Ngwa a jihar Abia.

Yan bindigar da rahotanni suka bayyana cewa sun kai su 50 sun sace makamai a ofishin yan sanda dake hanyar Umuhojima/MCC a karamar hukumar Osisioma a garin Aba.

Babban jami’in dan sanda dake kula da yankin ya ce yan bindigar sun kuma kone ofisoshin yan sanda biyu.

Sai dai DPO, CSP, Ajimo, bai bayyana sunayen yan sandan da aka kashe ba da kuma wuraren guda biyun da aka kone.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin da jami’ai biyu suka rasa ransu a Abayi Osisioma ragowar biyun an kashe su ne a ofishin yan sanda na Omoba.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Abia, Geoffrey Ogbonna, ya ce an kashe wasu daga cikin yan bindigar yayin musayar wutar a Omoba yayin da wasu suka tsere da makaman da suka sata a ofishin.

A ofishin yan sanda na Abayi/Umuojima Osisioma an lalata ababen hawa da gine-gine da dama da suke kusa da ofishin.

Gwamnatin jihar ta Abia ta mayar da martani kan harin da yan bindigar suka kai inda ta sanya ladan Naira Miliyan 1 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taima a kwato makaman da yan bindigar suka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here