Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram da dama tare da karbe iko da Garin Marte

0
103

Sojojin Najeriya sun samu nasarar shiga garin Marte inda suka kashe mayakan Boko Haram da dama wadanda suka yiwa garin tsinke a yan kwanakin nan.

Wata majiyar soji ta shaidawa PRNigeria cewa sojojin sun samu nasarar lalata nakiyoyin da mayakan suka dasa a hanya sannan kuma sun karbe kakkabe mayakan daga yankin.

“Sabuwar Marte tana cikin ikonmu tun karfe 3 na rana.” Inji wata Majiya.

A ranar Lahadin da ta gabaga ne dai babban hafsan sojan ƙasa na Najeriya ya ba dakarun Najeriya wa’adin sa’a 48 su kakkabe Boko Haram a ƙauyukan Marte da suka ƙunshi Kirenowa da kirta da Wulgo da Chikingudo a jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here