An cimma Matsaya Tsakanin KAROTA da Yan A daidaita Sahu

0
251

 

Jaridar Kano Focus ta wallafa labarin cewa, biyo banyan zaman gaggawa da aka gudanar tsakanin jami’an Hukumar KAROTA da kungiyar kwadago da kuma wakilan ‘yan adai-daita an cimma matsaya.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kungiyar Kwadago na jihar Kano kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai ranar Talata a Kano.

Kabiru Ado Minjibir ya ce an cimma matsaya masu tarin yawa da za su taimaka gaya wajen kawo karshen halin da ake ciki.

Matsayar da aka cimma

‘Yan Adai-daita Sahu za su biya harajin N100 kamar yadda doka ta tanada a kullum amma ba kamar yadda ya ke a bayaba.

Duk wanda zai biya harajinsa to dole ne ya yi Remiter karon farko domin a dauki bayanan sa a adana.

Haka kuma kowanne dan sahu zai biya, na farko a tsakanin makonnin biyu daga ranar 23 ga Fabrairu.

Haka kuma bayan anyi biyan farko za a ci gaba da biya na kullum-kullun ta wayar hannu ko kuma ta POS ba kamar a baya ba da sai anje banki.

Haka kuma duk wanda ya ke so zai iya biyan na kwana daya ko na sati ko kuma na wata-wata ko na shekara amma ba dole bane.

Haka kuma yana daga cikin abinda aka cimma, cewar shugabannin masu dan sahu za su yiwa mambobinsu bayani kuma za a janye yajin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here