Akwai ɗimbin masu ɗauke da cutar Korona a ɓoye a Najeriya – Bincike

0
164

 

Daga Junaid Idris Gezawa

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa,wani bincike a Najeriya ya nuna cewa hakikanin yawan masu ɗauke da cutar Corona a kasar ya zarta wanda hukumomin ke sanarwa nesa ba kusa ba.

Sakamakon binciken ya nuna cewa a birnin Legas kawai za a iya samun mutun miliyan huɗu da suka harbu da cutar kodayake a hukumance mutum dubu 54 ne aka tabbatar suna da ita.

Hukumar NCDC da ke ɗakile cutuka masu yaɗuwa da wata cibiyar binciken kiwon lafiya ne suka gudanar da binciken.

Kuma sun dauki samfurin jinin mutum dubu 10 daga wasu jihohi huɗu na Najeriya kuma binciken ya nuna duk mutum ɗaya cikin mutum biyar suna ɗauke da cutar.

An gudanar da binciken ne a jihohin Legas da Enugu da Nasarawa da kuma Gombe tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here