Wata Mata ta Nemi Kotu ta Raba Aurensu da Mijinta bayan Shafe Shekaru 10 ba tare da daukar ciki ba

0
121

Daga Junaid Idris Gezawa

Wata mata mai shekaru 30, Marwanatu Muhammad a yau Litinin ta roki kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Rigasa jihar Kaduna, ta raba Auren dake tsakaninta da mijinta Iliyasu bisa gazawarsa wajen yi mata ciki wanda zai kai ga ta samu haihuwa.

A karar da ta shigar, Matar ta ce Malam Iliyas bai yi mata cikin da za ta haihuwa ba tun lokacin da suka yi aure a shekarar 2011.

“Ya taba yin aure kafin yanzu amma matar ta barshi saboda rashin haihuwa. Nayi tunanin lamarin zai sauya a kaina amma nayi kuskure.

“Ina da lafiya, bani da wata matsala. Bana son ci gaba da zama dashi. Zan dawo masa da sadakin dubu 20, 000 da ya bani”, inji ta.

A martanin da ya mayar, Malam Iliyasu ya ce matar tasa ta rike masa kudinsa Naira 17, 700 kuma yana neman kotu ta karbo masa kudinsa.

Alkalin kotun, Malam Salisu Abubakar-Tureta ya bada umarnin kowannesu suje suyi gwajin lafiya don sanin inda matsalar take.

Alkalin ya nemi mai karar da ta rantse da Al’qurani mai girma cewa bata rike masa kudinsa Naira 17, 000 ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here