Shan Rake na Ƙara Ni’ima, Ƙarfin Sha’awa da Haihuwa Cikin Sauƙi – Masana

0
207

 

Wata likitan bangaren abinci a Babban Asibitin Agege dake jihar Legas, Misi Olufunmilola Adewumi ta bada shawara ga masu bukatar karin ni’ima da karfin sha’awa da su dinga shan rake.

ta fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Litinin, a birnin Lagos cewa, shan raken zai iya taimakawa mata masu matsalar ciwon mara samun sauki yayin daukar ciki da kuma samun saukin a lokacin haihuwa.

A cewarta, rake na dauke da isassun sinadaran kara ni’ima kamar nutrient da vitamin C da vitamin B2 da magnesium da iron da potassium da kuma phosphorus.

“Rake na dauke da sinadaran dake kare jariri a cikin mahaifiyarsa daga cututtuka da dama kamar su Spina bifida.

“yana kuma taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin gaba da kuma kara ruwan maniyyi.

“yana taimakawa wajen rage matsalar kankancewar gaba,” inji likitar.

Misis Adewumi ta Kuma ce baya ga wadannan fa’idojin, shan rake a kai a kai na taimakawa wajen takaita tasirin cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.

“yaa kan rage cututtukan dake da alaka da mafitsara da koda da kuma duwatsun ciki, musamman in aka hadata da lemon tsami da ruwan kwakwa,’’ inji ta.

Daga nan sai ta shawarci a rika shan akalla mililita 400 na raken a kullum
domin samun cikakkiyar fa’idarta.

Sai dai ta yi gargadi kan cewa shan raken fiye da kima na iya rikita ciki, ya kawo rama, ciwon kai da kuma yawan jin bacci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here