“Na Haifi Ɗa Amma ban taɓa Aure ba”, Jaruma Ejine Okoroafor, ta Karyata Google

0
150

Jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya, Ejine Okoroafor, ta bayyana cewa bata taba yin Aure ba.

Bangaren binciken bayanai na Google, wanda jama’a da dama ke amfani dashi wajen samun sahihan labarai a lokaci zuwa lokaci ne ya bayyyana cewa jarumar ta taba yin Aure.

Kodayake, jaruma Ejine Okoroafor ta bayyana cewa bayanan Google basu da tushe.

Ta ce, Google ya bada bayanin cewa tana da Aure wanda hakan karya ne.

“Bayanaina a Google ya ce ina da Aure. Bansan wane shasha ne ya rubuta a shekarar 2013 lokacin da na samu da a kasar Afrika ta kudu ba. Ban taba Aure ba. Na haifi da daya amma bantaba aure ba”.

Bayananta dai a shafin na Google ya bayyana cewa;
” Ejine ta auri Prince Wale sanan sun haifi yaro a watan Disamba na shekarar 2013 a kasar Afrika ta kudu”.

Ejine Okoroafor dai mai shirya fina-finai ce kuma yar kasuwa, ta shirya fim din “Trophy Wife”wanda Tchidi Chikere ya bada uamarni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here