An Janye Jami’an KAROTA daga Titunan Kano yayin da Yan Adaidaita Ke Yajin Aiki

0
153

A wani yunkuri na dakile arangama tsakanin jami’anta da matuka baburan Adaidaita Sahu, hukumar KAROTA ta janye jami’anta daga titunan jihar Kano.

Matuka baburan Adaidaita Sahu sun tsunduma yajin aikin gargadi yau Litinin a Kano bisa gazawar gwamnati na janye harajin Naira 100 da ta sanya musu.

Yajin aikin ya sanya mutane da dama tafiyar kasa a Kano, yayin da dalibai da sama basu je makarantu ba wasu kuma suka je a makare.

Jaridar SAHELIAN TIMES ta ziyarci wasu manyan titunana jihar Kano amma ba’a hango jami’an KAROTA ba kamar yadda suka saba tsayuwa.

A wasu yankunan yajin aikin ya koma rikici inda wasu ke dauke da sanduna da duwatsu suna farwa wadanda suka ki shiga yajin aiki.

A unguwar Sabon Titi, Sani Mainagge karamar hukumar Gwale, yan sanda sun tarwatsa matasan dake zanga-zangar bayan sun rufe hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here