Ƙungiyar Kwadago za ta yi Sulhu tsakanin KAROTA da Ƴan A daidaita Sahu

0
186

Kungiyar kwadago ta Najeriya(NLC) ta ce ta fara tattaunawar sulhu tsakanin matuka baburan A daidaita Sahu da hukumar dake kula da zirga-zirgar abababen hawa ta KAROTA bisa sanyawa matuka baburan harajin Naira 100 a kullum.

Rahotanni sun bayyana cewa, NLC na hada kai kungiyoyi masu zaman kansu don tabbatar da an samu dai-daito tsakanin bangarorin biyu domin wanzar da zaman lafiya a jihar.

Yayin da yake bayani a taron manema labarai a Kano, shugaban NLC na Kano, Comrade Kabir Ado Mijinbir ya bayyana yajin aikin a matsayin abin takaici a dai-dai lokacin da ma’aikata,dalibai da fasinjoji ke tafiya da kafafunsu ko kuma suke zaman gida saboda rashin abun hawa.

A yau Litinin ne dai matuka baburan A daidaita Sahu suka fara yajin aikin gargadi bisa gazawar gwamnatin jihar na janye harajin Naira 100 da ta sanya musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here