Yanzu-Yanzu: Ƴan Sanda Sun Kama Sanata Rochas Okorocha

0
324

Yan sanda a jihar Imo sun kama Sanata Rochas Okorocha a yau Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama tsohon gwamnan ne bisa zargin lalata ababen hawa na jami’an tsaro da na gwamnatin jihar tare kuma da balle ginin da gwamnatin jihar ta kwace na matarsa, Nkechi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai, Kwamishinan kasa na jihar, Enyinnaya Onuegbu ya ce gwamnatin jihar ta kwace ginin mallakar matar tsohon gwamnan wanda yake a titin Akachi.

Sai dai a yau Lahadi Okorocha ya shiga wajen ginin tare da gargadin Uzodinma da jami’an tsaro kan su bude ginin.

“Yayin da ya isa wajen, ya bukaci shiga rukunin gidajen, inda ya fadawa jami’an tsaron dake wajen cewa, babu wani umarni daga kotu na rufe ginin”, a cewar wata majiya.

“Ya jaddada cewa sai ya shiga ginin, kuma take ya balle wajen ya shiga.

“harbe-harben bindiga ya fara tashi yayin da hadiman gwamna Uzodinma suka isa wajen tare da yan sanda da kuma wasu rukunin mutane.

“Daga nan rikice ya barke. Daya daga cikin mutanen Okorocha ya samu rauni daga harbin bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here