Matuka Baburan Adai-daita Sahu Za su Fara Yajin Aiki Gobe a Kano

0
220

Matuka baburan Adai-daita Sahu sun yi barazanar shiga yajin aiki ranar Litinin a Kano bisa gazawar gwamnatin Kano na dakatar da Karbar harajin Naira 100 a kullum.

Rahotannin dai sun bayyana cewa, a ranar Asabar ne matuka baburan mai kafa uku suka taru tare fara raba takardu na shirin yin yajin aikin a ranar Litinin biyo bayan gaza samun matsaya tsakanin gwammati da shugabannin kungiyoyinsu.

Shugaban kungiyar matuka baburan na Kano, Alhaji Sani Dankoli ya ce matuka baburan sun yanke  shawarar shiga yajin aikin ne ba tare da Sahalewar kungiyar ba.

Dankoli ya bukaci matuka baburan na Adai-daita Sahu su dakatar da shirin yin yajin aikin inda ya ce yajin aikin zai shafi zirga-zirgar mutane da dama a jihar.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Laraba da ta gabata ne matuka baburan suka gudanar da zanga-zanga a manyan titunan jihar Kano inda suke jan hankalin gwamnatin jihar da ta janye harajin Naira 100 da t sanya musu a kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here