Rashin Samun Haɗin kai Daga Jama’a ne Babban Koma bayan da Mawakan Arewa Ke Samu -Matashi jr.

0
170

 

Daga Junaidu Idris Gezawa

A tattaunawar da jaridar PRIME TIME NEWS tayi da, Mawakin Hausa  Hip hop Abdulhadi Mustapha wanda akafi sani da Matashi Jr, ya bayyana cewa, rashin samun goyon bayan da mawakan Arewa ke samu shi ne babban cikas din da Mawakan yankin na Arewa ke samu.

Mawakin, wanda dan Asalin jihar Kano ne kuma haifaffen Gwammaja ya bayar da takaitaccen tarihin sa inda ya ce an haifeshi a Kano a Unguwar Gwammaja, ya yi makarantar primary a Giginyu primary school sanan ya yi karatun Sakandire a GSS Tarauni daga nan  kuma ya yi  karatun diploma a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano.

A bangaren Sana’a, Matashi jr ya ce ba iya waka kadai yake ba, shi kwararre ne kuma sananne a bangaren sana’ar aski. Sannan ya ce a bangaren waka kuma yazuwa yanzu ya yi wakoki da dama inda wakarsa ta “Majesty” ita ce wakar da ta zama bakandamiyarsa domin ita ce ta haskaka shi kuma ita ce wacce mutane sukafi so.

A wani bangaren kuma, matashi jr., ya ce ya samu kalubale daga bangaren iyaye sanda yafara waka sai dai daga bisani kuma iyayensa sun amince harsuna sa masa albarka.

A hirar da Jaridar PRIME TIME NEWS ta yi da shi, ya bawa mawaka yan uwansa shawara kan cewa su tsaya tsayin daka kan salo mai inganci bawai suyi tsaiwa irin ta gwamen jaki ko kuma kame-kamen salo ba.

Daga karshe ya ce a bangaren abinci Naman kaza shi ne abincin dayafi so sannan kuma yayi kira da masoyansa dasu ci gaba da bibiyarsa a shafinsa na sada zumunta musamman Instagram @Matashi Jr. tare dayi musu albishir da cewa su jira sabon kundin wakokinsa da zai saki nan bada jimawa ba inda ya kunshi wakoki harda na manyan Mawakan da suka shahara a Najeriya baki daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here