Ƙasar Benin za ta Haɗe da Najeriya a Matsayin Ƙasa Daya -Geoffrey Onyeama

0
322

Ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce shugaban kasar Benin, Patrice Talon ya bayyana bukatar kasarsa na hadewa da Najeriya.

Onyeama, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan tattaunawar Sirri da ministan harkokin wajen Benin, Aurelian Agbenonci, ya ce shugaban kasar ta Benin ya nuna bukatar yayin da ya ziyarci shugaban kasa Muhamamdu Buhari a makon da ya gabata.

“Shugaban kasar Benin ya ce kasar Benin na son zama jiha ta 37 ta Najeriya” inji shi.

“Zamu zama daya. Sun bukace mu mu hada kai mu samar da tsarin inganta alaka”.

Onyeama ya ce a ziyarar, shugabannin guda biyu sun tattauna kan yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu kan yadda zasu kawo karshen safarar kayayayki ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here