Matata na Wanke ni da Mari a Duk Sanda na Hukunta ƴaƴana – inj Wani Magidanci

0
336

Wani ma’aikacin gwamnati mai suna, Oyeniyi Oyedepo, a yau Juma’a ya fadawa kotu a Mapo dake garin Ibadan, ta yanke alakar Auren da suka shekara 14 da yi da matarsa, Iyabo, bisa karar da yayi cewa matarsa na tsinka masa mari a duk lokacin da ya hukunta ‘ya’yansu guda 4.

Mista Oyedapo, a karar da ya shigar ya ce matarsa ta mare shi saboda ya yiwa ya’yansa gyara.

“Iyabo ta riga ta bata zamanmu na aure. A kodayaushe tafi nunawa ‘ya’yanmu so.

“A duk lokacin da na hukunta daya daga cikin ‘ya’yanmu idan yayi ba dai-dai ba, Sai Iyabo ta tsinka min mari.

” Bata biyaya gareni kuma tana da fushi”inji Mista Oyedebo.

Iyabo wacce yar kasuwa ce ta amince da bukatar Sakin da mijin nata ya nema.

“Eh! Na mare shi. Amma saboda ya dakeni kuma ya ce nabar gidansa.

“Sannan Oyedepo neman mata yake, bana son sa yanzu”, inji Iyabo.

Shugaban kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce auren nasu zai ci gaba idan suka sa hakuri a ransu.

Sannan ya gayyaci yan’uwan ma’auratan don su shiga tsakani.

Sannan ya daga karar zuwa 6 ga watan Afrilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here