Akwai yiwuwar Sake Bullar Cutar Ebola a Najeriya – NCDC

0
141

 

 

Daga Junaid Idris Gezawa

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka a Najeriya ta NCDC ta saka Najeriya a “mataki na tsakatsaki” na yiwuwar ɓullar annobar cutar Ebola bayan ɓullar cutar a ƙasar Guinea.

NCDC ta bayyana haka ne a shafinta na intanet, tana mai cewa an ɗuki matakin ne saboda kusancin Guinea da Najeriya da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

“Ganin irin kusancin Najeriya da Guinea da kuma sauran ƙasashen Afirka ta Yamma, an saka Najeriya a mataki na tsakatsaki na ɓullar annobar cutar Ebola,” a cewar NCDC.

Ebola ta ɓulla a Guinea ranar 14 ga watan Fabarairu, inda aka samu mutuwar mutane a yankin N’zerekore.

Mutum bakwai ne suka kamu bayan sun halarci jana’izar wata ma’aikaciyar jinya ranar 1 ga Fabarairu, a cewar NCDC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here