Sheikh Gumi zai Ziyarci Garin Kagara Inda aka Sace Dalibai a Safiyar Yau

0
103

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi alkawarin ziyartar garin Kagara dake jihar Niger inda aka sace wasu dalibai da safiyar yau Laraba.

Yayin da yake magana bayan ziyartar gwamnan Niger, Alhaji Abubakar Sani Belle, Shekh Gummi ya bayyana lamarin a matsayin abin rashin jindadi.

Ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa jihar Kebbi amma ya yanke shawarar dakatawa a Minna babban birnin jihar Niger don tattaunawa da gwamnan kan lamarin.

Malamin ya ce wannan ne karo na farko da ya ziyarci jihar, inda ya kara da cewa tattaunawar da yayi da gwamnan zata bawa gwamnati damar samun hanyar magance matsalar tsaro.

Makwanni biyu da suka wuce, Sheikh Gumi ya tattauna da yan bindiga a maboyarsu, inda ya roke su su ajiye makamansu.

Sannan ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi yan bindigar afuwa.

Sai dai wasu masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai sun ki amincewa da shawarar na yiwa yan bindiga afuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here