Sha’aban Sharada Ya Zargi Ganduje da Haifar da Rikici a Jam’iyyar APC a Kano

0
234

Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar birni, Sha’aban Ibrahimm Sharada ya soki shugabancin jam’iyyar a jihar bisa kokarin hana shi sabunta rijistar zama dan jam’iyyar.

Sha’aban Sharada ya yi zargin ne yayin da yake yiwa manema labarai jawabi yayin ziyarar da ya kai makarantar Sakandire ta Salanta don sabunta rijistar tasa amma bai samu koda mutum daya ba na kwamitin yin rijistar a wajen.

Dan Majalosar wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar wakilai, wanda kuma yake tare da dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar birni, ya zargi gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da da hannu cikin masu bashi wahala a jam’iyyar.

Gwamna Ganduje da Sha’aban Sharada dai an shata layi tun lokacin zaben fidda gwani na yan takarar shugabancin kananan hukumomi a jihar.

Sannan ya soki Gwamna Ganduje bisa cefanar da kadarorin gwamnati.

A wani bidiyo da yayi yawo a kafafe sadarwa na zamani an hango sha’aban Sharada na nuna takaicinsa kan yadda gwamnan ke siyar da filin masallacin Idi, makabartu, makarantu da kasuwanni.

Dan majalisar wanda ke bayani cikin fushi ya yi zargin cewa gwamnan bai kyale koda asibitoci ba.

“Sun san cewa zan zo amma sai suka bar wajen bayan sun samu umarni daga sama amma koma mene, zan ci gaba da biyayya ga APC da kuma ubangidana shugaban kasa Buhari”, inji Sha’aban.

” Suna yin duk wannan ne saboda na alakanta kaina da Buhari sai dai za su fadi nan bada jimawa ba”.

“Ina biyayya ga jam’iyya, a matsayin wakiki a majalisar wakilai, ina cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyya; banga dalilin da zai sa a umarci kwamitin sabunta rijista a mazabata su bar wajen ba saboda kawai nazo na sabunta rijista ta. Ban chan-chanci haka ba.

Dan majalisar ya kuma musanta batun cewa zai bar jam’iyyar ta APC.

“Bazan bar jam’iyyar maigidana ba, wadanda ke adawa damu a jam’iyyar suna yin hakane saboda suna son barin jam’iyyar nan gaba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here