Kamfanin TEC ya tabbatarwa da Abba Gida-Gida cewa Gadar Kofar Nasarawa za ta Shekara 80 da Ingancinta

0
213

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano na Jam’iyyar PDP, Abba K Yusuf(Abba Gida-Gida) ya rubuta wasika ga kamfanin TEC, kamfanin da yayi aikin gina gadar sama ta kofar Nasarawa, inda ya nemi kamfanin ya gudanar da bincike kan ingancin gadar da kwarinta daga lokacin da aka kammala ta zuwa yau biyo bayan zargin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi na cewar gadar ta fara zaizayewa.

A wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Abba Kabir Yusuf, Ibrahim Adam, tsohon kwamishinan ayyukan a lokacin gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci kamfanin ya gudanar da bincike mai zurfi kan ingancin gadar.

A martanin da kamfaninn na TEC ya mayar ga wasikar Abba Gida-Gida ya kara tabbatar da cewa an gina gadar bisa inganci kuma tana da garanti na tsawon shekaru 80 tunda daga shekarar 2015.

Injiniyoyin kamfanin da sauran kwararru sun tabbatar da cewa gadar na da inganci kuma bata fara zaizaye wa ba.

A farkon watan nan ne dai kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mallam Muhammad Garba, ya bayyana cewa za su rushe gadar saman ta kofar Nasarawa saboda ta fara zaizayewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here