Ana Zargin Dalibin Jami’ar FUD ya kashe Kansa Bayan Sun samu Sabani da Budurwarsa

0
257

Wasu rahotanni dake fitowa daga jami’ar tarayaya dake garin Dutse(FUD) na cewa ana zargin wani dalibi mai suna Abubakar Bashir
Wanda aka fi sani da Emiratus ya rasa ransa bayan ya sha guba sakamakon rashin jituwa da ya faru tsakaninsa da budurwarsa.

Dalibin dai dan Asalin jihar Kano ne wanda ke zaune a Unguwa uku dake karamar hukumar Tarauni kuma yana ajin karshe a jami’ar.

Wani dalibi kuma daya daga cikin shugabannin dalibai a makarantar  Ahmad Muhammad Amoeva, ya tabbatarwa da jaridar PRIME TIME NEWS faruwar al’amarin inda ya bayyana cewa marigayin ya dade da shan gubar kuma har an kwantar dashi a Asibiti.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga mahukanta makarantar kan batun abinda yayi sanadiyar rasuwar dalibin wanda ke karatu a sashin koyan ilimin kimiyar lissafi mai lamba FSC/17/MTH/2003.

Sai dai daliban makarantar da dama sun tabbatarwa da jaridar PRIME TIME NEWS faruwar lamarin yayin da hoton marigayin da wacce ake zargin budurwarsa ce ke yawo a shafukan sadarwa na zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here