An Kama Babban Jami’i a Hukumar Hisba tare da Matar Aure a Dakin Otel a Sabon Gari

0
1043

Rundunar Hisba ta jihar Kano ta tabbatar da labarin cewa yan sanda a unguwar Nomansland sun kama daya daga cikin manyan jami’anta mai suna Sani Nasidi Uba Remo, bisa zargin samunsa da matar Aure a dakin Otel a yankin Sabon gari.

Wata majiya mai tushe daga ofishin yan sanda na Nomanslanda ta shaidawa jaridar SAHELIAN TIMES cewa sun kama Remo ne bayan sun  karbi korafi daga mijin matar. Sannan an kama shi ne yayin da suke tare da matar a dakin otel din dake sabon gari.

Mataimakin Kwamandan Hisaba yaje ofishin yan sandan don karbar belin Kwamandan da aka kama, inda da farko yan sanda suka ki bada belinsa sai dai bayan tattaunawa, yan sanda sun mayar da batun zuwa shelkwatar hukumar Hisba don yin cikakken bincike.

A martanin da ya mayar babban kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya tabbatar da cewa sun kadu matuka da jin labarin. Sannan ya ce an kafa kwamitin bincike kan batun kuma an bawa kwamitin wa’adin kwanki 3 ya kammala aikinsa.

Sani Remo dai shi ne jam’in dake kamo karuwai kafin a mayar dashi bangaren kaman Almajirai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here