Ra’ayi: Dalilin Da ya Sa Jagora Rabiu Kwankwaso Ya Kafa Nasara Radio- Herssern Umar

0
155

 

 

Daga, Herssern Umar (Hassanul Basari)

Kwankwasiyya redcap rangers vP

Jagora Rabiu Kwankwaso mutum ne mai matuqar kishin yankin daya fito a ciki, ma’ana Arewa.

Tunanin Kwankwaso da hangen nesan sa ya wuce yadda wasu suke daukar sa, wato mutum ne da Allah ya bawa kaifin basira da zurfin tunani akan abubuwan da kan iya zuwa su dawo a wannan kasa.

Yadda abubuwa suka kasance a Nigeria da sanin yadda jiya take da kuma bambancin da aka samu yau shine ya bawa Kwankwaso hango abinda gashi yazo muna gani.

Yanzu an wayi gari rayuwar Hausawa da Fulani sunfi komai araha a kudancin Nigeria, kullum kashe mu suke kuma kamar sun kashe banza.

Dalili kuma shine duk wata kafar yada labarai ta wannan kasa idan ka bincika zaka ga mallakin mutanen kudu ce, kuma da wannan kafofin sadarwa suke yin magana kuma da ita suke cimma manufofin su.

Mutanen mu da aka kashe a wadannan kwanaki Allah ne kadai yasan yawan adadinsu, amma ba’a sanin yawan wadanda ake kashewa saboda basa yadawa tunda sune sukai barnar kuma manufar kenan dama.

Idan muka dauki misali da zanga zangar #Endsars da kuma wacce akai a Arewa za kaga kamar kawai muryar ‘yan kudu kawai ake ji a wannan kasa dama duniya.

Wannan duk yana da alaqa ne da yadda suke yada buqatunsu har su jawo hankalin kasa da duniya baki daya, har sai an biya musu buqatunsu koda kuwa ba duka ba.

Anan Arewa kuwa idan banda tashoshin shirya finafinai irinsu Arewa 24 da ire-irensu za kaga bamu da kafofin sadarwa irin na wadancan mutane.

Kishin Kwankwaso da hangen nesan sa shine ya bashi dama har Allah yasa ya kafa wannan gidan Radio na Nasara.

Idan bamu manta ba akwai abubuwa da dama da suka faru na cin zarafi ga mutanen Arewa a can Kudun, kuma Kwankwaso shine kadai wanda ya rinqa kai wannan dauki a duk tarin Shugabannin da muke dasu a Arewan.

Kwankwaso ya fahimci wannan hanyar ta kafa kafofin yada labarai sune kawai hanyar kawo karshen irin wadannan cin kashi da mutanen kudu suke mana.

Idan da Shugabannin Arewa suna da tunani da hangen nesa irin na Kwankwaso da tuni Arewa tayi nisa a wajen irin wannan cigaban da kudu take dashi na kafafen sadarwa.

Sai dai kash! Shugabannin Arewa sun dade da siyar da kansu wajen manyan da suke kudu, yanzu a kwanakin nan sai kashe mutanen mu ake amma duk sunqi magana saboda siyasar su, amma sai gashi Ganduje dasu Malam Shekarau har cewa suke 2023 mulki a barwa mutanen kudu kawai saboda suna kwadayin kujerar mataimakin Shugaban Kasa.

Ya rage namu yanzu mu fahimci masu kaunar Arewa da kishin ta, da kuma mutanen da basa kishin mu amma sunfi kowa son su mulke mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here