PDP ta Nemi Rundunar ‘Yan Sanda ta Tuhumi Abdullahi Abbas Bisa Kalaman Tunzura Jama’a

0
143

Jam’iyyar PDP ta rubuta wasika ga babban sufe janar na yan sanda, Mohammed Adamu, inda take neman a tuhumi shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas bisa kalaman batanci.

“Ku hukunta duk wanda kuka gani yana yunkurin satar kuri’a yayin zaben 2023. Ku dau mataki da hannunku ba abinda za’ayi. Ina umartarku da ku hukunta duk wanda kuka gani gaban akwatu yana kokarin yin mugudin zabe, hukuncina ne, babu abinda zai faru.

“Ina kira ga matasan jam’iyyarmu su adana makamansu akwai lokacin amfaninsu”, cewa Abdullahi Abbas yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano.

Yayin da yake mayar da martani kan kalaman, shugaban jam’iyyar PDP na Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce sun mika takarda ga babban sufeton yan sanda na kasa da hukumomin da abin ya shafa.

“Bamu yi mamaki ba, halayyarsa ce haka ta bayyana kalaman tunzuri. Wannan kalaman batanci ne.

” gare mu wannan barazanar baza ta hana mutanen Kano zabar wadanda suke so ba”, inji shi.

Abdullahi Abbas dai ya saba bayyana ire-iren wadannan kalaman na tayar da tunzuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here