Ranar Masoya: Ƴan Matan Jos sun ce sun Fi son Kyautar Kuɗi fiye da Fure yayin da Samari ke korafin mata basa basu Kyauta

0
184

A yayin da ake bikin ranar masoya ta duniya, wasu mata a garin Jos sun ce sun fi bukatar “Kyauta mai ma’ana” fiye da kyautar kati, furen soyayya da alewa wadanda aka saba bada su a ranar ta masoya.

A wani bincike da aka yi tsakanin mata masu aure da marasa aure ya nuna cewa sun bi nuna sha’awar yin bikin ranar a gidajensu kan zuwa wuraren shakatawa sakamakon annobar Korona.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya rawaito cewa Ranar Masoya rana ce da masoya ke bayyana soyayyarsu ga wadanda suke kauna tare da gaisuwa da rabon kyaututtuka wanda hakan zai kara dankon soyayya.

Ajala Omusa, ta cd: “Bana bukatar fure na ranar Masoya, hakan baya nuna soyayya sosai a gareni, furen soyayya gare ni ba wani abu bane, ina son wasu kyaututukan da zan dinga gani kowacce rana wadanda su dinga tunamin rana ta musamman.”, inji Misis Omusa.

Ana ta bangaren Amy Casaidy ta ce, ” bana bukatar fure, kawai ina son hutawa a gida kamar shirya taron cin abinci a gida tare da samun lokaci na musamman da mijina, saboda bama samun lokaci sosai saboda yanayin aiki”, inji ta.

Gift Udom kuwa cewa ta yi tafi bukatar mijinta ya fita yawon shakawata da ya’yansu ya barta a gida tana hutawa.

“Hutawa a gida ba tare da yara ba na tsawon wasu awanni, zai taimaka sosai kuma hakan zai sa ‘ya’yan su samu lokacin zama da babansu”.

Sannan ta ce sakon kyautar kudi zai sa ta farin ciki a ranar.

Wasu mazan da suka zanta da kamfanin dillacin labarai na NAN sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda basu samu kyaututtuka daga maza ba inda suka ce sun samu kyautar rigar Singlet da wanduna ne kadai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here