Matasan Yarabawa Sun Ƙona Masallaci da Shaguna 50 na Hausawa a Jihar Oyo

0
504

Yan daban yarabawa na ci gaba da kone shagunan yan Arewacin Najeriya dake zaune a kasauwar Sasa karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo duk da dokar hana fita da aka sanya.

An kone shaguna fiye da 50 da masallaci a safiyar ranar Lahadi.

Yayin da yake zantawa da jaridar DAILY NIGERIAN a yau Lahadi, shugaban kungiyar yan kasuwar Sasa, Usman Yako, ya ce ana ci gaba da sace kayan jama’a a safiyar ranar Lahadi.

“An kone shagunan madinka 50 a safiyar yau. An kuma kone masallacin dake kusa da shagunan”, inji Alhaji Yako.

Wani Bahaushe mazaunin Sasa, Danlami Abubakar ya fadawa jaridar ta DAILY NIGERIAN cewa gwammatin jihar bata daukar matakan da ya dace don kare rayukansu.

Ya ce an ankarar dasu cewa yan daba na shirin kai hari ga yan Arewa dake zaune a Sabo-Ibadan.

“A wannan safiyar, mun samu rahotan cewa yan daba na shirin kawowa mutanenmu hari a Sabo-Ibadan. Idan ba’a dau matakin gaggawa ba rikicin zai yadu zuwa wasu yankunan”, inji shi.

“Ina kira ga gwamnatin tarayya ta kawo mana dauki, ta kawo karshen kashe-kashe da lalata dukiyoyi”.

Wata majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa, babu isashen tsaro a gidan Sarkin Saa, Haruna Maiyasin, wanda ke ajiye yan arewa dake gudun hijra su dubu 6.

An kashe a kalla mutane 10, yayin da mutane 70 suka ji raunuka inda mutane 30 suka bace a harin da aka kaiwa Hausa a kasuwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here