Ranar Masoya: ‘Ku Sanya Ido Kan Ƴaƴanku’,Ƙungiyar Kiristoci ta Shawarci Iyaye

0
192

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya(CAN), Apostle Joshua Akinyemiju, ya bukaci iyaye su sanya idanu a kan ‘ya’yansu don tabbatar da basu aikata abinda ba dai-dai ba a bikin ranar masoya da ake kira Valentine’s Day.

Akinyemiju ya bada shawarar ne yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a yau Asabar a Ibadan.

“Iyaye suna soyayya ga ‘ya’yansu, , su sanar da ‘ya’yansu cewa Annabi Isah shine gidauniyar soyayya.

“Wannan so yakamata mu kwaikwaye shi a tsakaninmu.

“Ranar Valentine, rana ce ta so, ta nuna soyayya, da nuna farin ciki da soyayya.

“Rana ce da kowa zai shiga bikinta da kuma kallon dalilin da yasa muke a yan’uwa”, inji shi.

Sannan ya bukaci shugabannin coci-coci da su yi amfani da bikin ranar masoyan wajen yin wa’azi kan soyayya ranar Lahadi.

“Kirista ba zai yi ikirarin yana son Allah ba yayin da kuma yake kin dan’uwansa mutum.

“Rana ce ta samun sulhu tsakanin ma’aurata, yan’uwa da sauron su”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here